Kungiyar yaki da kwari dake yada cututuka a Najeriya ta ce kimannin mutane dubu uku suke mutuwa kowacce shekara sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wajen wani taron manema labarai a birnin Ikko inda take bayyana bukatar tashi tsaye haikan wajen shawo kan matsalar beraye a matsayin hanyar magancea zazzabin Lassa a yankunan karkara, musamman idan aka kwatanta da adadin mutane da suke mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar a nahiyar Afrika.
Shugaban kungiyar Ayo Ogunyedale ya bayyana cewa, ana iya samun wannan cutar da bera ke yadawa a ko’ina. Ya kuma ce cutar tafi yaduwa da rani kasancewa bera da sauran kananan halittu dangin bera suna yawo a sawwake da rani ko’ina.
Mr. Ogunyedale yace alamun cutar suna kama da cutar zazzabin cizon sauro ko shawara, da suka hada da zazzabi da ciwon kai da ciwon kirji da kuma mura da tari. Cutar kuma bisa ga cewarshi, tana haddasa zawo da kasalar jiki.
Ya bayyana cewa, jama’a zasu iya kare kansu daga kamuwa da cutar ta wajen kula da muhallinsu da kawar da bera da kuma kawar da tarkace.