ZAUREN VOA: Batun Yadda Tinubu Ya Nada Mata 9 Cikin Ministocinsa, Kashi Na Karshe - Oktoba 01, 2023

Medina Dauda

Medina Dauda

Wannan shiri na karshe inda manyan baki, da Ali M.Ali dan Jarida kuma daya daga cikin masu magana da yawun Kungiyar Kamfe din Shugaban Kasa na Jamiyyar APC, da Madam Ene Ede yar gwagwarmayar kwato wa mata yanci kuma shugabar Kungiya mai zaman kanta mai suna EQUITY ADVOCATE da yar siyasa Hajiya Bilkisu Ibrahim, an tattauna batutuwa da suka jibanci kujerun Ministoci 9 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba mata a Najeriya, wannan lamba ya yi daidai da kashi 18% cikin 100 na mukaman, duk da cewa bai kai kusan kashi 35% da mata suke nema ba, amma sun ga kokarin shugaban kasa, tare da kira gare su da su tabbata sun taimaka wa mata musamman wadanda suke sansanonin gudun hijrah da su da 'ya'yansu kusan fiye da miliyan 2 da rashin tsaro ya raba su da matsugunansu.

A yi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN VOA