ZAUREN VOA: Yadda Mata Ke Tallafawa Juna A Kamaru, 09 Afrilu, 2023

Medina Dauda

Wani dattijo da ya halarci zaman zauren  mai suna Abubakar Adamu, ya amince cewa iyalan mazajen mata da suka rasa mazajensu, ba sa taimakawa marayu da ake barin matan da su.

A cikin wannan shirin, 'yar jarida kuma wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka a Kamaru Maimouna Sadou ta fadi irin taimakon da mata ke yi wa kansu a cikin mawuyacin halin da suka tsinci kansu inda sukan tara kudi da kansu daga aljihansu domin tallafa wa juna. A yi sauraro lafiya.

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN VOA: Yadda Mata Ke Tallafawa Junansu - 14'26"