ZAUREN VOA: Yadda Mata Ke Fafutuka A Fagen Siyasar Najeriya, 23 Afrilu, 2023

Medina Dauda

Matan sun bayyana tarihin siyasarsu da yawan shekaru da suka kwashe suna gwagwarmaya a wannan fagge da maza suka fi yawa.

Tattauna wa ce da mata 'yan siyasa a Najeriya. An samu bakuncin Hajiya Heebah Ireti Kingibe wacce ta kwashi shekaru 20 tana neman kujerar Sanata a Birnin Tarayya, sai bana ta samu sa'ar cin zabe a karkashin Jamiyyar Labour Party, da Hajiya Khadijah Abdullahi Iya wacce ta tsaya takarar kujerar Gwamna a Jihar Neja a karkashin Jamiyyar APGA. Da Barista Hassana Ayuba Mairiga Tula, sai 'yar gwagwarmayar kwato wa mata yanci Hajiya Balaraba Abdullahi. A yi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN VOA: Fafutukar Da Mata Ke Yi A Fagen Siyasar Najeriya - 15'05"