ZAUREN MATASA: Yadda Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari - Yuli 24, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin zauren matasa ya sauka a garin Dan Umaru da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya, mai albarkar matasa manoma.

Matasan sun taru a zauren inda su ka koka da cewa ga dai damina ta kankama amma 'yan bindiga sun hana su shiga gonaki da ke nesa da gari. Matasan na bukatar dauki don kar hakan ya zama barazana ga samar da abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayiwa.

Saurari shirin a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN MATASA: Yadda Damuna Ta Kankama Amma Miyagun Iri Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari - Yuli 24, 2023