ZAUREN MATASA: Ya Kamata Mu Tashi Mu Karbi Mulki Daga Hannun Tsofaffin 'Yan Siyasa - Fabrairu 27, 2023

Nasiru Adamu El Hikaya

Matasa a zauren da mara bayan wasu manyan mata a shekaru sun baiyana irin mafarkin da su ke yi cewa in an samu shugabanci nagari kasar za ta koma kan kykakyawar turbar nasara da cigaba.

Mahalrata zauren sun karfafa ra’ayin cewa lokaci ya yi da tsoffin jami’an siyasa na gwamnati za su yi ritaya su bar fagen ga masu jini a jika.

Duk da wahalhalun da a ke fuskanta da kuncin talauci, Hajiya Asabe Nasarawa ta yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN MATASA: Ya Kamata Mu Tashi Mu Karbi Mulki Daga Hannun Tsofaffin 'Yan Siyasa.mp3