Shirin wannan makon ya tattauna da matasa a birnin Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya don duba irin gudummowar da zasu bada wajen inganta lamuran tsaro a jihar da ke fuskantar barazanar 'yan bindiga, musamman a yankin karamar hukumar Isa da Sabon Birni.
Matasan sun ba da shawarar cewa doka ta yi halinta a duk lokacin da aka samu wani da hannu a wajen kawo fitina a jihar.
Kazalika, a cikin shirin matasan sun bayyana wasu abubuwa da su ke ganin in an bi za a samu maslaha a kan wannan kalubalen.
Saurari shirin:
Your browser doesn’t support HTML5