ZAUREN MATASA: An Ayyana Dokar Ta-Baci A Yankin Karamar Hukumar Karu Na Jihar Nasarawa, Agusta, 29, 2022

Nasiru Adamu El-Hiyaka

Matasa mazauna karamar hukumar Karu sun bayyana yadda dokar ta shafi rayuwarsu ta yau da kullum musamman masu kananan sana'o'in da su ke yi don samun kudin shiga.

MATASA

A cikin shirin na wannan makon mun sauka a yankin karamar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa inda hukumomi su ka ayyana dokar hana yawon dare don dakile miyagun iri yayin da bayanan sirri ke cewa 'yan ta'adda na kwararowa yankin daga wasu sassan da su ke fuskantar barazana.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti: