ZAURAN MATASA: Tattaunawa Kan ‘Yan Sara Ruka A Minna Da Ke Jihar Neja, Kashi Na Biyu, Agusta 08, 2022

Nasiru Adamu El-Hiyaka

Cigaba da tattaunawa a zauren matasan da ya zauna a Minna fadar gwamnatin jihar Neja inda matasa su ka tattauna kan illar wasu ajin matasan da kan aikata miyagun laifuka da kan kai ga asarar rayuka da dukiya.

Sabon shirin ya duba yadda wasu iyaye su ke kare ‘ya’yan su, ko da an same su da shiga wannan mummunar dabi’a ta rashin da’a.

Zauren ya ba da shawarar aiki tare tsakanin iyaye da duk hukumomin da su ke ladabtar da matasan ciki kuwa har da malaman makaranta.

Your browser doesn’t support HTML5

ZAURAN MATASA: Tattaunawa Kan ‘Yan Sara Ruka A Minna Da Ke Jihar Neja