Kasar Cote’d Voire wadda taci wasanta na farko a gasar cin kofin duniya, na shirin gamuwa da Colombia, domin nasara a wannan wasa ka iya kaita ga zagaye na biyu.
A matsayin kungiyoyin na kasashe biyu wadanda kasashensu basu cigaba ba, Cote’d Voire da Colombia zasu zage damtse na gani basu bar damar zuwa zagaye na biyu ta wuce su ba, saboda kungiyoyin guda biyu zasu yi wasa a garin Brasilia Alhamis mai zuwa.
Yanzu kungiyoyin biyu duk sun samu nasara a wasanninsu na farko a rukunin group C, saboda haka nasara a wasan dake tafe zai tabbatar da tafiyar daya daga cikin kungiyoyin zuwa zagaye na biyu.
Idan Cote’d Voire tayi nasara, to zai zama karo na farko da taje wannan zagaye, saboda bata samu hayewa ba a shekarar 2006 da 2010 a lokuta biyu kawai da kasar ta taba zuwa gasar cin kofin duniya.
Ita kuma Colombia ta taba zuwa zagaye na biyu a shekara ta 1990, inda aka cinye ta a wasan farko a zagayen. Sai dai yanzu kalubalenta kawai shine rashin tauraron dan wasanta Radamal Falcao wanda ya samu matsala a gwiwarsa, amma duk da haka kungiyar ta cinye Girka da ci 3 da babu.
Your browser doesn’t support HTML5