Zasu Fafata Wajan Zama Zakaran Kwallon Kafa Na Afirka

Riyad Mahrez

Dan wasan gaba na Leicester City dan kasar Algeria Riyad Mahrez, da dan wasan kasar Gabon mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Pierre Emerick Aubameyang su ke kan gaba a cikin jerin Sunayen ‘yan wasan da zasu fafata wajan lashe lambar yabo na zakaran kwallon kafa na Afirka a bana (BBC African Football of the Year).
Shi dai Mahrez ya jagoranci Kungiyarsa ta Leicester City, a yayin wasannin Firimiya lig na 2015/2016 inda ya zurara kwallaye har guda goma sha bakwai ya kuma tai maka aka jefa guda goma sha daya, abinda ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Firimiya na 2015/2016, har ila yau yana cikin tawagar ‘yan wasan kasar Algeria.
Shi kuwa Aubameyang ya jefa kwallaye har guda ashirin da biyar a shekaran 2015/2016 a gasar lig na kasar Jamus inda a wannan shekarar ma ya zurara kwallaye goma sha daya a wasanni daban daban da ya buga wa Kungiyar ta Borussia Dortmund.
Aubameyang, na cikin manyan ‘yan wasan da zasu haskaka a gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka wanda za'a yi a kasar sa ta Gabon a watan Janairu 2017.
A cikin jerin Sunayen akwai Yaya Toure na Manchester City da Mane na Liverpool.