Gwamnatin soja ta Burkina Faso ta sanarda janye jakadanta na Ghana tare da gurfanar da jakadan Ghana a Burkin Faso sakamakon ikrarin da shugaban kasar Ghana, Nana Addo, yayi a gefen taron Amurka da kasashen nahiyar Afrika a Washignton cewa Burkina Faso ta dauko sojojin hayar Rasha wato Wagner domin yaki da ta'addanci akudancin Burkina Faso abin da ke barazana ga tsaron Ghana musamman yayin da kasar Ghana ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ke yi Ukraine.
Shugaban Ghana Nana Addo ya ce "a yau an girke dakarun haya na kasar Rasha a iyakokinmu ta arewa. Burkina Faso ta kulla yarjejeniya da dakarun haya na Wagna tare da Mali ina da imanin cewa an bai wa dakarun mahakar ma'adinai da ke kudancin Burkina Faso a matsayin ladar aiki. Girke dakarun a kudancin Burkina Faso mai makwabtaka da Ghana abin damuwa ne sosai musamman a wannan lokacin da mu ka yi Allah wadai da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine" inji shi.
Wasu masharhanta kan harkar tsaro a Ghana na ganin wannan ikirari da shugaban Ghana yayi ka iya haifar da matsalar diflomasiyya tsakanin Ghana da Rasha, ba ma ita Burkina kadai ba. Adib Sani mai sharhi kan harkar tsaro ya ce "Ghana da Burkina na da alaka, musamman ta musanyar bayanan sirri, amma wannan al'amri ya sa Burkina Faso ba za ta yarda da Ghana ba; kazalika an samu tsamin dangantaka tsakanin Ghana da Rasha" inji shi.
Shi kuwa tsohon jakadan Ghana a kasar Guinea, Excellency Musah Shariff Nuhu Na Layya, na ganin kowace kasa na cin gashin kanta, amma kasancewar Ghana na makwabtaka da Burkina Faso kamata yayi a tura tawaga zuwa Burkina Faso domin ganin an daidaita tsakanin kasashe biyun.
Wakilin muryar Amurka ya tuntubi shugaban majalisar tsaro a yankin da ke iyaka da kudancin Burkina Faso, wato Hamza Amadu, a inda ya ke cewa a shirye jami'an tsaron Ghana da suka hada 'yan sanda da jami'an shige da fice tare da sojoji, suke su dakile duk wani yunkurin shiga kasar Ghana da wasu 'yan ta'adda za suyi muddan an koro su daga Burkina Faso.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams daga Accra, Ghana:
Your browser doesn’t support HTML5