Zargin Cristiano Ronaldo Da Laifin Fyade Ya Dau Sabon Salo

Dan wasa Cristiano Ronaldo

A kan zargin aikata fyade da akeyi wa Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da yayi wa Kathryn Mayorga, a wani otel da ke Las Vegas a 2009,
yanzu haka 'yan sanda a birnin Las Vegas ta Amurka suna bukatar a ba su kwayoyyin halittar (DNA) na Cristiano Ronaldo, domin cigaba da gudanar da bincike a kan zargin.

Sai dai Lauyan Cristiano mai suna Peter S. Christiansen ya shaida wa manema labarai cewa, wannan bukatar kawo kwayoyyin hallita ba wani abu ba ne.

Jaridar (Wall Street Journal) ta wallafa cewa an aika takardar bukatar hakan ne zuwa wata kotu da ke kasar Italy.

Tun a farkon wannan zargin Ronaldo ya musanta cewar bai aikata hakan ga
Kathryn Mayorga ba. inda Lauyan sa ya bayyana cewa har yanzu dan wasan yana kan bakarsa, na cewar abun da ya faru a Las Vegas a 2009, ba fyade ba ne, da amincewar ta, don haka ba abun mamaki ba ne idan an ga kwayoyin halittar Ronaldo,

Wata Mujallar (Der Spiegel) ta kasar Jamus ce ta fara wannan tonon sililin ta hanyar wallafa zargin da Ms Mayorga ta yi, bayan ta kai kararsa wajen 'yan sanda a Las Vegas bayan faruwar lamarin.

Inda aka bayyana cewar a shekara 2010, Ms. Mayorga ta yi wata yarjejeniyar sirri da Ronaldo a kan ya biyata dala $375,000 domin kada ta tona masa asiri.

Yanzu haka dai 'yan Sanda na ci gaba da bincike dan samun gaskiyar lamarin.