ZARGIN BACEWAR NAIRA MILIYAN 150 A JAHAR NAIJA NA TAYAR DA KURA

  • Ibrahim Garba

Tambarin hukumar EFCC

Zargin bacewar kudi ko rashin bacewarsu ya janyo murza gashin baki tsakanin 'yan jam'iyyar APC da PDP a jahar Naija.

An shiga karce kasa bayan zargin bacewar Naira miliyan 150 a gwamnatin Jahar Naija, ta yadda Fadar Gwamnatin jahar da jam’iyyar APC mai mulki ke ta kokarin gano bakin zaren game da wannan zargin. Al’amarin ya dada sukurkushewa ne bayan da wasu kafafen yada labarai su ka ce sun ji kakakin APC Mr. Jonathan Batsa na kira ga gwamna Abubakar Sani Bello da ya hanzarta gano yadda aka yi Naira miliyan 150 din su ka bace bat a gidan gwamnatin na jahar Naija.

Shi kansa Mr. Batsa y ace kira kawai su ka yi ga gwamnan cewa kamar yadda Shugaba Buhari y ace ba zai yi hulda da mahandama ba, shi ma gwamnan jahar ta Naija kar ya yadda mahandama su rabe da shi; amma babu wata maganar Naira miliyan 150. Shi ma Sakataren Yada Labarai na gwamnan jahar ta Naija Dr. Ibrahim Doba y ace bai ma san inda labarin miliyan 150 ya samo asali ba. Y ace karya ce kawai.

Duk da yak e tuni gwamnatin ta Jahar Naija da jam’iyyar APC su ka musanta wannan zargin, su kam ‘yan adawa sai cigaba da kirayen-kirayen a hanzarta gano kudaden su ke yi. Wani tsohon hadimin tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu mai suna Honorabul Yahaya Ability y ace bayanan ‘yan APC din na cin karo da juna don haka da walakin kuma ya kamata ma gwamnatin ta yinkuro don yin abubuwan da su ka zarce na gwamnatocin da su ka gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

ZARGIN BACEWAR NAIRA MILIYAN 150 A JAHAR NAIJA NA TAYAR DA KURA - 2'56''