Zanga Zangar Farko a Nijar, Bayan Sakin Jagororin Fafutuka

Dandazon jama'ar da suka fita zanga zangar farko a Yamai, Jamhuriyar Nijar, bayan sakin shugabannin masu fafutuka, 09-09/18 Sule Mumuni Barma

"Na maimaita wannan magana, don kusan cewa, wannan kokowa (fafutuka) inda aka dakatar da ita a ranar 1 ga watan Maris, daga nan za ta ci gaba." Inji Moussa Tchangari, daya daga cikin masu jagorar wannan tafiya.

Dubban jama’a sun fita kan tituna a birnin Yamai da sauran jihohin kasar a ci gaba da watsi da dokar harajin 2018.

Hakan na faruwa ne duk da hukumomi na cewa tsari ne da zai taimaka a samu kudaden gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin fararen hular da ke adawa da dokar harajin ta 2018 ke gudanar da zanga zanga bayan da kotu ta sallami wasu gaggan shugabannin wannan tafiya a ranar 24 ga watan Yulin.

An sake su ne, bayan shafe watanni 4 a kurkuku saboda zargin gudanar da zanga zanga ba da da izinin hukuma ba.

Ayarin masu zanga zangar ta wannan Lahadi ya yi tattaki ne daga "Place Toumo" zuwa Dandalin "Place de la Concertation."

"Na maimaita wannan magana, don kusan cewa, wannan kokowa (fafutuka) inda aka dakatar da ita a ranar 1 ga watan Maris, daga nan za ta ci gaba." Inji Moussa Tchangari, daya daga cikin masu jagorar wannan tafiya.

Rahotanni na cewa jama’a sun fito kan tituna a manyan biranen jihohi 8 ciki har da Diffa da ke karkashin dokar ta baci sanadiyar matsalar Boko Haram.

Masu lura da al'amuran sun ce hakan manuniya ce da ke tabbatar da cewa tasirin zagayen da shugabannin wadanan kungiyoyi suka gudanar a makon jiya ya karbu.

"Daga nan Yamai har zuwa Diffa, Agadez, Maradi, Zinder, Tileberi, babu inda mutane ba su fito ba." Inji Mounkaila Halidou, wani shugaban masu fafutukar.

Haka zagaye na 17 na abin da jami’an fafutuka ke kira JAC ya samu halartar dumbin mata.

Kungiyoyin kawancen, sun kudiri aniyar sake fitowa a ranar 23 ga watan Satumba domin kalubalantar hukumomi akan maganar dokar harajin ta 2018, duk da cewa gwamnatin ta sha ankarar da ‘yan fafutukar cewa bakin alkalami ya riga ya bushe.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga Zangar Farko a Nijar, Bayan Sakin Jagororin Fafutuka - 2'15"