Karamar hukumar mulkin ta Isa da ke gabashin jihar Sokoto na daya daga cikin yankunan da suka dade suna fama da matsalar 'yan bindiga, masu kai hare-hare suna kisan jama'a, satar dabbobi da sace mutane domin karbar kudin fansa.
Lamarin ya kara ta'azzara a 'yan kwanakin nan, sakamakon kwararowa da 'yan bindigar makwabciyar Zamfara suke yi, biyo bayan luguden wuta da sojin Najeriya suke yi a sansanoninsu.
Wannan yanayin ne ya sa wasu matasa a garin Isa, shelkwatar karamar hukumar mulki ta Isa, suka gudanar da wata zanga-zanga, domin nuna fushinsu.
To sai dai kuma zanga-zangar ta dauki sabon salo, yayin da wani bangare na masu zanga-zangar suka kai farmaki tare da kona gidajen kwamishinan lamurran tsaron jihar, Kanal Garba Moyi mai murabus, da kuma na sarkin Gobir duk a cikin garin na Isa.
Da yake wadanda ke da hannu ga afkawa gidan suna hannun jami'an tsaro, wakilin Muryar Amurka ya tuntubi wani dan garin kuma shugaban rundunar adalci a jihar Sakkwato, Bashir Altine Guyawa ko me ya ingiza matasan yin hakan, sai ya danganta al'amarin da matsalar rashin tsaro, kamar yadda ya yi bayani cikin sauti.
A nata haujin rundunar 'yan sandan Najeriya, ta bakin kakakin ta a Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ta tabbatar da aukuwar lamarin .
Wakilin Muryar Amurka ya kuma samu zantawa da sarkin Gobir na Isa Nasiru Ahmad na biyu, wanda aka bubbuge fadar sa, wanda ya bayyana mamakin dalilin kai farmaki a gidansa, duk da kasancewar ba shi ne ke rike da ragamar sha'anin tsaro ba.
"A matsayin sarki, babban abin da zan iya yi shi ne ba da shawara, kuma kowa yana ji ina ta rubutawa gwamnati kan matsalolin al'ummata na sha'anin tsaro. Bayan wannan ba abin da zan iya yi kuma," in ji basaraken na Isa.
Har wayau wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kwamishinan tsaron wanda aka Kona gidajensa amma ya ce ba zai maganta ba saboda ‘yan sanda na binciken batun.
Sai dai wasu majiyoyi da ke da alaka da kwamishinan tsaron, sun ce ana zargin shugaban karamar hukumar mulkin ta Isa, Abubakar Yusuf Dan'ali da shirya zanga-zangar da kuma kona gidajen kwamishinan.
Masu zargin sun ce shugaban karamar hukumar yana son daukar fansa ne akan tuhumar da ake yi masa na taimakawa 'yan ta'adda, bayan da aka kama wata mota da ake zargin ta shi ce, da ake amfani da ita waje kai wa 'yan bindiga abinci da makamai a jihar Zamfara.
To sai dai a martanin da ya mayar, shugaban karamar hukumar ya musanta wannan zargin, yana mai cewa shi ma labari kawai ya samu cewa ana zanga-zanga a Isa, alhali yana ma a cikin garin a lokacin.
"Kawo zargi na, sanadiyyar cewa an kama mota ta tana kai abinci wani wuri ga 'yan ta'adda, bayan ni ina yaki wadannan 'yan ta'addar, to wannan ya zama cin mutunci da cin zarafi a gare ni," ta bakin Dan'ali.
Ya kara da cewa wadanda suka shirya zanga-zangar da aka kama su, sun tabbatarwa jami'an tsaro cewa a kashin kan su ne suka gudanar da ita, illa dai wasu bata-gari ne suka shigo suka sauya al'amura ba daidai ba.
Masu sharhi akan lamuran yau da kullum dai na ganin sakacin hukumomi ne akan rashin tsaro yasa karamar magana ke zama babba, har jama'a ke nema wa kansu mafita.
Matsalar rashin tsaro dai a iya cewa ta kure tunanin kowa a Najeriya, sai dai da matakan da ake dauka yanzu a wasu jihohi tare da farmaki da soji ke kaiwa ‘yan ta'addar akwai fata na samun saukin matsalolin.
Ga rahoton Muhammad Nasir daga Sakkwato:
Your browser doesn’t support HTML5