Ranar ma’aikatan ko kuma May Day rana ce da aka saba gudanar da zanga zanga kamar ta wannan shekara. Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga zanga dake gudanar da taro a Taksim Square a Istanbul, wurin da aka zubda jinni a wadansu tarukar ranar ma’aikatar a baya.
Tashin hankali a Turkiya ya kara ta’azzara biyo bayan wani karamin rinjayi da shugaba Racep Tayyib Erdogan ya samu a zaben raba gardama a watanr da ya gabata inda shugaban ya lashe wasu madafun ikon kasar.
A jiya Litinin yan sanda sun kama mutane sama da 200.
A kasar Venezuela kuma zanga zangar ma’aikatar ya zama tashin hankali inda aka samu masu ra’ayi da kuma masu kin jinin gwamnati suna gudanar da zanga zanga. Jami’an tsaro a babban birnin kasar Caracas,sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan matasar dake jifansu da duwatsu da suke zanga zangar kin jinin gwamnatin gurguzu ta shugaba Nicholas Maduro.