Zanga Zangar Lumana A Garin Tsafe Ta Dauki Sabon Salo

Lamarin ya soma ne da zanga-zangar lumana, inda daruruwan ‘yan gudun hijira, akasari mata da yara da ma tsofaffi, suka tattaru a garin Tsafe ta jihar Zamfara, suka kuma toshe babban titin Gusau zuwa Zariya, lamarin da ya yanke zirga-zirga a titin.

Masu zanga-zangar na nuna damuwarsu ne akan jerin hare-hare da ‘yan bindiga suka kwashe tsawon kimanin makwanni 2 suna kaiwa, a garuruwan da ke gabashin karamar hukumar mulkin ta Tsafe, wanda yayi sanadiyyar salwantar rayuka da dama, wasu daruruwa kuma suka yi kaura daga muhallansu.

San Turaki wani mazauni garin Tsafe ne, ya kuma bayyanawa shashen hausa na muryar Amurka yadda lamarin ya fara.

Sai dai daga bisani lamarin ya dauki sabon salo, bayan da masu zanga-zangar suka kwarara zuwa cikin garin, suka kuma cinna wuta tare da kona sakatariyar karamar hukumar ta Tsafe kurmus, har ma da wasu gidaje da motocin al’umma.

Na nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara akan lamarin hakan bai samu ba, to amma kwamishinan watsa labaran jihar Sanda Muhammad Danjari, yace tuni da aka shawo kan matsalar, bayan da aka tura jami’an tsaro.

‘Yan gudun hijirar sun kwararo ne a garin na tsafe daga garuruwa fiye da 15, da ke fuskantar hare-hare a kusan kowace rana ta Allah.

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga Zangar Lumana A Garin Tsafe Ta Dauki Sabon Salo 3'16"