To amma 'yar awaren kungiyar ta Joy Ajeroh tana cewa a'a ba zasu shiga yajin aiki ko zanga-zanga ba akan karin farashin man fetur.
Wannan zanga zanga bata samu fitowar mutane da yawa ba idan aka kwantata da zanga zangar shekarar dubu biyu da goma sha biyu da kungiyar tayi akan karin farashin mai din.
Kwamred Ibrahim Khalil bai yadda cewa hakan koma baya ba ne ga kiran kungiyar saboda 'yan Najeriya da dama sun kushewa zanga zangar. Khalil shi ne ma'ajin kungiyar yace 'yan Najeriya su fahimta uwar kungiyar kwadago bata na rigima da shugaba Muhammad Buhari ba ne. Amma yace 'yan jari hujja sun yiwa shugaban kakagida. Suna neman su kwaceshi daga hannun talakawa. Mutane su gane wannan gwagwarmaya ce ta kare shugaban domin kada azzaluman kasar su kwaceshi.
To saidai bangaren kungiyar da ya bare ya nuna takaicin zanga zangar. Jami'in bangaren Kwamred Nasiru Kabir yace abun da kungiyar kwadagon dake zanga zanga karya take yiwa 'yan Najeriya.
'Yan kwadagon sun gana da 'yan majalisar kasar amma babu alamar dawo da farashin man saidai a soma maganar kara albashi.
Dattawan arewa da suka hada da Justic Mamman Nasir sun fito sun goyi bayan gwamnatin Buhari da matakan da yake dauka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5