Zanga Zangar Kasar Iraki Na Dada Kazancewa

  • Ibrahim Garba

Birnin Bagadaza ya turnike da hayakin zanga zanga

Yayin da kasar Iraki ke kokarin murmurewa daga bala'in ISIS da sauran fitintinu, sai ga shi wata zanga-zangar nuna rashin gwamsuwa da manufofin gwamnati na nemar ta sake durkusar da kasar.

Jami’an tsaron Iraki sun yi harbi da harsasan gaske kan masu masu zanga-zanga a jiya Asabar, su ka kashe 19 daga cikinsu, baya ga wasu da dama da su ka ji wa raunuka a birnin Bagadaza kawai ma, a rana ta biyar ta wannan zanga-zanga kan manufofin gwamnati, wadda ta girgiza kasar baki daya.

Adadin wadanda su ka mutu a birnin Bagadaza da wasu birane da dama a kudancin Iraki, ya kai wajen 100. Akasarin masu zanga-zangar sun yi biris da kiraye kirayen gwamnati da shugabannin addinai, na su kai zuciya nesa. A birnin Bagadaza, masu zanga-zanga sun yi ta arangama da jami’an tsaro a unguwanni da dama, su ka yi ta kona tayoyi a kan tituna.

Masu zanga-zangar sun fadada bukatunsu daga batun samar da ayyukan yi da abubuwan more rayuwa – kamar su ruwan sha da wutar lantarki – su ka kara da kiran da a kawo karshen almundahana a wannan kasa mai arzikin man fetur, wadda ke dauke da mutane kimanin miliyan 40.