'Yan sanda a Faransa sun jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a shahararren dandalin nan na Champs - Elesees. Masu zanga-zangar na nuna damuwarsu ne kan tsadar rayuwa a Faransar.
'Yan sanda sun ce masu zanga-zanga akalla 1,500 ne su ka bazu kan titunan birnin Paris, kuma an kama a kalla 127 daga cikinsu.
A shirinta na tinkarar mako na hudu na wannan zanga-zangar, kasar ta Faransa ta rufe hasumiyar Eiffel da kuma wasu sanannun wuraren yawon bude ido, sannan ta sa dubban jami'an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana.
An rufe shaguna da dama a birnin na Paris kafin zanga-zangar ta yau Asabar don kauce ma fushin masu zanga-zangar da kuma wasoso.
Tun da aka fara zanga-zangar a watan jiya saboda tsadar man fetur, mutane hudu sun mutu a wasu al'amura masu nasaba da zanga-zangar.