A Hong Kong, dubban masu zanga zanga ne suka bazama akan tituna a jiya Asabar a yankin, wanda ke karkashin ikon China, domin yin zanga zangar neman a inganta tsarin Dimokradiyya a yankin.
Kamfanin Dillancin Labaran Reuters, ya ruwaito cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla akan masu zanga zangar da suka lalata 'yar karamar hanyar dogo a yankin.
Zanga zangar ta jiya ta samo asali ne bayan da masu goyon bayan China suka yayyaga sakonnin adawa da gwamnati da aka mammana a jikin bango a sassan birnin, wanda ake wa lakabi da “Lennon Wall.”
Shi dai rikicin siyasar na Hong Kong ya samo asali ne, tun bayan da hukumomin yankin suka gabatar da wani kuduri da zai samar da dokar da za ta rika ba da dama ana tura wadanda ake tuhuma da aikata laifi zuwa China, domin a yi masu shari’a, matakin da masu zanga zanga suka ce sam ba zai yi wu ba.