A Ethipia, ko Habasha,mazauna garuruwa akalla 12 a kudancin kasar sun fantsama kan tituna suna zanga-zangar gwamnati ta sabunta laisisn hakar ma'adinai ga wani kamfani da suke zargin aikace-aikacensa yana shafar lafiyar su.
Zanga-zangar da ake yi a yankin Oroma mai fama da rigingimu,suna zargin sabunta lasisin wani kamfani mai suna Mohammed International Research and Organization, ko MIDROC har na tsawon shekaru 10.
Zanga zangar ta biyo matakin da hukumomi suka dauka ranar Jumma'a 27 ga watan Afrilu a makon jiya, na sabunta lasisin kamfanin wadda yake aikin hakar zinari tuna wajajejn 1990. Kamfanin na wani hamshakin attajiri ne wadda yafi sauran takwarorinsa a duk fadin nahiyar arziki mai suna Shiekh Mohammed Hussein al-Amoudi.
Shi dai mai kamfanin yana hanun hukumomin Saudiyya ne tun cikin watan 11 kan zargin cin hanci da rashawa.