Sabon ministan harkokin wasanni da matasa na Najeriya, Barrista Solomon Dalung, ya bayyana cewa zai bayar da hankalinsa ga batun kyautata halin da matasan Najeriya ke ciki, duk kuwa da cewa bai shiga ma'aikatar ya ga halin da take ciki ba.
A lokacin da yake tattaunawa da wakilin VOA Hausa, Umar Faruk Musa, Mr. Dalung yace akwai bambanci kan batun yadda za a iya yin gyara ga wanda yake kallo daga waje, da kuma wanda yake kallo daga ciki. Don haka zai fi so sai ya shiga ya ga abubuwan da ake da su a kasa, kafin ya yanke shawarar abinda zai yi.
Minista Dalung ya ce, "tun da yanzu ne aka rantsar da mu, to sai mun shiga gidan (mun) duba, mu san mecece ke kasa, daga nan sai mu san inda za mku tinkara, muyi masa gyara."
Amma dai ya ce "harkar matasa na bukatar a sa hankali (a kai) domin a cece su, kuma a horar da su, su zamo shugabanni na kwarai gobe."
Your browser doesn’t support HTML5