Najeriya, nada jami’oi, fiye da dari da arbain, kama daga na Gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi da masu zaman kansu.
Kuma kimanin dalibai miliyan biyu ne ke zaman jarabawar neman gurbin shiga jami’a a kowace shekara inda kimani miliyan daya ke samun nasara a jarabawar.
Amma dalibai dubu dari biyar ne kawai jami’oin kasar ke iya dauka kamar yadda Ibrahim Usman Yakasai, darakta mai kula da hulda da jama’a da kuma watsa labarai na hukumar dake kula da jami’oin, Najeriya, ya bayyawa muryar Amurka.
Ya kara da cewa hukumar su yanzu tana da yarjejeniyar tsakaninta da hukumar dake kula da jarabawar daukar daliban jami’a (JAMB) da kuma hukumar dake kula da masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta inda hukumomin zasu sami sunayen da adadin daliban da hukumar ta baiwa kowace jami’a damar dauka.