Jim kadan bayan samun labarin hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke akan zaben gwamna na shekarar 2019 a jihar ta Zamfara, jama’a da dama sun fantsama kan tituna suna murna.
Wasu da dama, akasari magoya bayan ‘yan takarar jam’iyyar APC da ake yiwa lakabi da G-8 da suka gabatar da karar, da kuma na jam’iyyar PDP, sun bayyana farin cikinsu akan lamarin. Sun yi godiya ga Allah bisa ga hukuncin da kotun kolin ta yanke, inda suke cewa Allah shi ke bada mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so don haka wannan ya zama darasi ga sauran ‘yan siyasa.
Sai dai kuma da alama bangaren jam’iyyar APC a jihar ya rungumi kaddara, a ta bakin Sani Gwamna Mayanci, wani jigon jam’iyyar, kuma na hannun daman gwamna mai barin gado.
Kotun kolin dai ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC mai mulkin jihar ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwanin ba, lamarin da ya sa bata cancanci zabukan da aka ayyana ta lashe a zaben da aka gudanar na watan Maris din shekarar nan ta 2019 ba.
Sirajo Garba, na daga cikin lauyoyin jam’iyyar APC da suka halarci zaman yanke hukuncin kotun a birnin tarayya Abuja. Yace kotun ta sallami kara ta farko da aka daukaka kuma ta bada umarni a ba wadanda ake kara Naira miliyan goma.
Tuni da kotun ta bada umarnin rantsar da ‘yan takarar jam’iyyar da ta zo na 2 a yawan kuri’u a zaben da ya gabata, kwanaki 5 kacal kafin ranar 29 ga watan Mayu.
Saurari cikakken rahoton Murtal Faruk Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5