Zambiya Na Tunanin Halalta Tabar Wiwi

Zambiya ta shiga cikin jerin kasashen Afirka da suka ba da izini ko kuma suke tunanin halalta tabar wiwi har zuwa wani mataki, ya yin da halalta miyagun ƙwayoyi irin waddannan, sannu a hankali suke canzawa suna samun karbuwa wajen saka hannun jari sakamakon amfanin su ta bangaren kiwon lafiya.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Dora Siliya, a wani taron Majalisar ministocin na musamman a ranar 4 ga Disamba, ta ba da izinin samarwa da fitar da tabar wiwi domin karfafa tattalin arzikin kasar, wajen anfani dasu a bangaren magunguna.

Ya yin da wannan zai sanya kasar Zambiya ta zama kasa ta baya-bayan nan da za ta canza matsayarta game da maganin don bunkasa tattalin arzikinta, a sanarwar Siliya ba ta bayyana ko an hallalta yin amfani da tabar wiwi ba a Zambiya.

Lesetho ita ce kasar Afirka ta farko da ta fara halaltta tabar wiwi, kuma a wannan shekarar na 2017, Afirka ta Kudu da Zimbabwe sun bi sawu. Lesotho cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya, duk da haka a yanzu, tabar wiwi itace ta uku a bangaren samun kudaden shiga da ya habbaka tattalin arzikin kasar.