Zamanin Turawan Mulkin Mallaka Yafi

Tsohon Ministan kudi Alhaji Adamu Ciroma, ya nuna mamakin yadda Gwamnatoci a matakai ke gaza biyan albashin ma’aikatansu wanda ya zayyana haka da cewa zalunci ne.

Ya furta haka ne a wurin rufe Tafsirin bana a Masallacin Uthman Bn Amfan Wuse 2 Abuja, daf da inda ‘yan ta’adda suka tada bom bara da yayi sanadiyar mutane da dama.

Yace idan ya tuna aikin Gwamnati a lokacin Turawan mulkin mallaka na Ingila, ya Kanye juyayin zamani yau, yana mai cewa “ A zamana na yanzu ina mamakin cewa wadanda Gwamnatocin kasar nan suka kirasu suka basu aiki suna aikin nan akan sharadin za’a biyasu wata wata sai gashi yau ma’aikacin Gwamnati zai yi aiki watani fiye da ukku ba’a biyashi ba wannan zalunci ne wanda baka iya gina Gwamnati akan abunda yake da zalunci.”

Mai gudanar da Tafsirin Sheikh Hussaini Zakaria, ya bikaci Gwamnatin Buhari, da kada ta juya baya kan soke shingayen bincike na Sojoji.

A nasa bangaren Sheikh Surajo na Alhaji Sabo Keffi, na Masallacin Izala, a Maitama, yace a guji gaggawa ga sauyin da Gwamnatin Buhari tayi alkawari, yace “ A daina gaggawa barnan da aka kwashe shekaru da yawa ana yi zai bazai gyaru cikin watani ba.”