An gudanar da wasan tseren ne na tsawon kilomita takwas inda matasa daga sassan birnin Yamai suka halarci wasan domin karrama ranar zaman lafiya ta duniya.
A bangaren mata an baiwa mutane goma na farko da ke kan gaba a wannan tsere inda wacce ta zo ta daya ta samu kyautar jaka hamsin da kofi yayin da mai bi mata ta samu kyautar jaka talatin.
Haka zalika mutane goma ne suka samu tikwici a bangaren maza, kana an baiwa guragu maza da mata damar nuna bajinta akan kekunansu inda suka nishadantar da mutane.
‘‘Wannan taro an yi shi ne domin a shaidawa duniya ya kamata a zauna lafiya, ya kamata duk wata husuma da aka samu ta kare.’’ In ji Sakataren hukumar wanzar da zaman lafiya ta kasar Nijar, Abdu Bukar Ibrahim.
Ga karin bayani a wannan rahoto na Souley Moumouni Barmha :
Your browser doesn’t support HTML5