Zaman Lafiya Shine Damuwarmu Kafin Zabe

Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima a Maiduguri. (File Photo)

Gwamnan jihar Borno ya nuna damuwar shi dangane da yadda rashin tsaro ya yawaita a yankin.

Gwamnan jihar Borno Kashin Shattima Ibrahim, ya bayyanar da cewar gwamnatin shi na iya bakin kokarinta ta ga cewar an samu zaman lafiya a jihar da ma kasar baki daya, ganin yadda zabe ya karato yanzu damuwar su shine yaza’ayi a gudanar da zabe a jihar batare da wani damuwaba.

Yace wannan tashe tashen hankullan ba zasu sa akiyin zabe a wadannan yankin ba, ganin cewar anyi zabe a wasu kasashe da ke fama da yake yake, amma duk da haka ba a ki yin zabeba, kamar su Abganistan, Libya, Irak da dai sauransu don haka maganar zabe hakin ‘yan Najeriya ne wadanna da ke a gida da waje.

Don haka babu wani dalili da zai sa a hanama yan kasa suyi zaben a bun da suke so ba bisa ga wannan dalilin babu wata hujja da zata sa a hanamusu zabe. Yace babban damuwar shi yanzu shine yaza’ayi a samu zaman lafia a yankisu su taimakama al'uma, ba wai maganar zabe ba, wanda yasan da cewar idan da rai da lafiya to zabe zai gudana a yanki wanda yanzu abun da yarage zuwa ga zabe kwanaki kadan ne, don haka babu wanda ke da tabbas ko ze kai lakacin zaben.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaman Lafia Kamin Zabe - 3'12"