Manhajar WhatsApp na daya daga cikin manhajoji da aka fi sani ta tura sakonnin nan-take dake taimakawa mutane tura sakonni a fadin duniya.
Yayinda manhajar ke samar da saukakakkiyar hanyar hada masu amfani da ita da abokansu, da 'yan uwa, wata sa'in ta kan ba wasu mutune da mutum bai sani ba damar tura maka sakonni da kuma wuce gona da iri ko keta ka'idar jama'a.
Wannan ya sa kamfanin ya fito da wata dabara da mutane zasu iya dakile damar samun sakonni daga wani/wata da basu bukata.
Mutum na iya toshe sakon wasu mutane ba tare da sun san yayi ba, kuma manhajar ba zata sanar da su cewa sakon ya isa ko kuma bai isa ba.
To ko ta yaya za a iya toshe wani ta WhatsApp bayan kun yi musayar sakonni?
Ga masu amfani da wayar iPhone, da farko zasu shiga manhajar WhatsApp sai su bude sakonnin wanda suke so su toshe. Daga nan kuma sai a danna sunan mutumin daga sama, sannan daga can kasa kuma akwai inda aka rubuta Block sai a danna wurin.