Zahra Musa Galadima – Daliba ce da ta samu damar zuwa kasar Masar domin karatun aikin Likitanci da kwarewa a fannin 'Anesthesia.' Da farko ta so ne ta karanci wani kwas daban bayan ta fara karatu a jami'ar Al’qalam ta hanyar samun gurbin tallafi na 'Scholarship' inda ta nemi Micro Biology.
Bayan ta fara karatu a jami’ar Al’qalam fannin 'Chemistry' sai ta ji bata son kwas din, sai ta sake neman jami’ar KUST wato Wudil inda ta samu gurbi har ta fara biyan kudin makaranta, sai kuma ta nemi tallafin karatu a kasar Misra a karkashin gwamnatin jihar Kano. Ta samu gurbin karatu a fannin aikin likitanci na Anesthesia.
Malama Zahra ta ce, sai ta hakura da gurbin karatun da ta samu a jami’ar Wudil dake Kano, saboda ta je kasar Masar ta fara karatu, duk kuwa da cewar ta samu canjin sheka daga abinda ta so ta karanta tun da farko.
Kasancewar ba abunda ba ta so ta karanta ba ne, amma kuma, karatun kasar na da sauki. Ana bayanai yadda ya kamata sabanin yadda yake a nan gida Najeriya inda a cikin aji guda, akan samu fiye da dalibai 100.
Ta ce, a can kasar Masar, da zarar basu fahimci abunda ake koya musu ba, sukan yi korafi kuma a canza musu malami, ko a sauya harshe daga Larabci zuwa harshen Turanci domin su fahimta.
Your browser doesn’t support HTML5