Yau sabuwar majalisar wakilan Amurka za ta yi zabe a zagaye na hudu don zabar wanda zai shugabanci majalisar.
‘Yan Republican da suka karbe ikon majalisar sun gaza zabar wanda zai maye gurbin Nancy Pelosi.
Hakan ya sa aka dage zaman majalisar zuwa Laraba bayan da aka yi zabe har zuwa zagaye na uku ba tare da an kai ga gaci ba.
Dan majalisar wakilai Kevin McCarthy mai wakiltar jihar California da yake takarar kujerar, ya gaza samun adadin kuri’a 218 da ake bukata.
Wasu ‘yan Republican da adadinsu ya kai kusan 20 sun ki marawa McCarthy baya a ranar Talata a duka zagayen da aka yi.
Rahotanni sun nuna cewa ba a taba ganin irin wannan dambarwa a siyasar Amurka ba, inda da a ga wani ya fadi zaben shugaban majalisar wakilai a zagayen farko tun a shekarar 1923.
‘Yan Republican 20 da suka ki zaben McCarthy, sun kadawa dan Republican Jim Jordan kuri’unsu ne.
Jordan, wanda ke wakiltar jihar Ohio, bisa rahotanni ya nuna cewa, bas hi da burin zama shugaban majalisar wakilan.
A zagaye na uku da aka kara McCarthy ya samu kuri’a 202 yayin da Jordan ya samu 20.
McCarthy na bukatar karin kuri’a akalla 16 idan har yana so ya zama shugaban majalisar wakilan.
Bisa al’ada, zaben shugabannin majalisun dokokin Amurka shi ne abu na farko da ake yi a ranar da aka fara zama, amma a wannan karo abin ya ci tura.