A yau Talata masu kada kuri’a a jihar Georgia dake kudancin nan Amurka suna zaben sabon dan majalisar wakilai, a wani zabe na musamman da ka iya zama zakaran-gwajin-dafi ga ‘yan jam’iyar Republican a karkashin mulkin shugaba Trump, yayin kuma da jam’iyar ke kokarin ganin ta ci gaba da zama mai rinjaye a majalisar.
Irin makudan kudaden da jam’iyun Republican da na Democrat suka kashe a wannan zabe, ya yi nuni ga irin muhimmancin zaben, inda aka kashe sama da Dala miliyan 50, adadin kudin da ya fi kowane yawa a tarihin zaben majalisar wakilai a Amurka.
Dan takarar jam’iyar Democrat, Jon Ossof mai shekaru 30, wanda a da tsohon ma’aikaci ne a majalisar, ya kasance yana wannan takara ne a karon farko, wanda a zaben watan Aprilu na farko ya samu nasara, amma kuma ya gaza samun adadin kuri’un da ake bukata.
Abokiyar hamayyarsa Karen Handel mai shekaru 55 ta taba rike mukamin sakatariyar gwamnatin jihar ta Georgia.
Duk wanda ya lashe wannan zabe, shi zai maye gurbin Tom Price, dan Republican din da ya lashe zaben da ratar kashi 23 a watan Nuwamba, gabanin shugaba Trump ya nada shi a matsayin wanda zai jagoranci ma’aikatar lafiya da harkokin jama’a na yau da kullum.