Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta gudanar da wani taron horas da jami’anta kan sabbin dabaru na tabbatar da tsaro a zabukan gama gari da za a gudanar a fadin kasar a shekara mai gabatowa.
Kimanin manyan ma’aikata 100 daga jihohi biyar na yankin kudu maso gabas ne rundunar ‘yan sandan kasar ta tattaro don horaswa ta wuni guda da ta shirya a Inugu, babban birnin jihar Inugu.
Da ya ke jawabin bude taron, Mista Mike Ogbuekwe da ya wakilci gwamnan jihar, Mista Ifeanyi Ugwuanyi, ya jaddada bukatar zurfafa tunani wajen samar da dabaru na zamani da za su taimaka gaya wajen kare al’umma a lokutan zabe.
Ya ce, “Muna ganin wannan horaswa a matsayin albarka a garemu a jihar Inugu, kuma muna kyautata zaton cewa da kasancewarku, zamu more wani yanayin lumana a shekarar 2023, kamar yadda muka mora a lokutan zaben da suka wuce. Muna sa ran cewa a karshen horaswar, yanayin tsaro zai ingantu a jihar Inugu da ma yankin kudu maso gabas baki daya fiye da yadda ya ke yanzu.”
Kwamishinan rundunar ‘yan sanda ta jihar Inugu, Malam Abubakar Lawal, a hirarsa da manema labarai, ya bayyana muhimmancin shirya irin wannan taron gabannin zabukan badi.
Ya ce, “Yayin da muna shiri don zaben shekarar 2003, muna bukatar irin wadannan shirye-shiryen don kara mana basirar gudanar da zaben yadda ya kamata. Ba za mu so wani ya ji wani tsoro ba saboda kullum muna kara kokari ne na ganin an yi sahihin zabe a shekara mai zuwa.”
Daga bisani, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 9, Isaac Akimoyede, ya yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da su kawar da duk wani tsoro su fito zabe, yayin da hukumomi ke ci gaba da bunkasa hanyoyin gudanar da zabukan badi lami lafiya.
Saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5