A Najeriya, Jamiyyun adawa uku wadanda aka yi zaben Shugaban Kasa tare da su, a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu na wanan shekarar, sun bayyana matakan da za su dauka bayan da hukumar zabe ta kasa ta ayyana dan takarar Jamiyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Abuja, Nigeria —
Jamiyyun da suka bayyana korafin su tareda shaida wa duniya irin matakan da zasu dauka akan sakamakon zaben, su ne Babban Jamiyyar adawa ta PDP wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a karkashinta, sai Jamiyyar Labour ta tsohon Gwamnan Jihar Anambara Peter Obi, sannan Jamiyyar SDP wacce ta bayyana ra'ayi na daban da na sauran jamiyyun.
Dan takarar Jamiyyar PDP Atiku Abubakar ya ce ya kwashi shekaru da dama yana ganin zabuka a Najeriya, amma bai taba ganin zabe mara sahihanci irin wannan zaben Shugaban kasa na shekara 2023 ba, domin an tafka kurakurai masu yawa, saboda haka ya zama wajibi a kalubalanci sakamakon zaben gadangadan.
Atiku ya ce saboda haka ne ya ke son ya ja hankalin duniya ga kurakurai da aka yi tare da jan hankalin hukumar zabe domin ta gyara aiyukan ta. Atiku ya ce bai tsayar da shawarar shigar da kara a kotu ba amma zai tattauna da lauyoyin sa da kuma shugabanin jamiyyar PDP kafin ya dauki mataki. Atiku ya ce zai sadaukar da rayuwarsa wajen inganta dimokradiyya a kasar domin ya kwashi sama da shekaru 30 yana siyasa kuma ta zama tamkar wani bangare na rayuwarsa.
Shi kuwa mai magana da yawun Jamiyyar Labour Dokta Yunusa Tanko ya ce Jamiyyar Labour wacce tsohon Gwamnan Jihar Anambara Peter Obi ya tsaya a tutarta, ta na da tabbacin cewa ita ce ta ci zaben shugaban kasa, kuma za ta nuna hujjojinta, inda ta shirya tsaf domin shigar da kara kotu.
Yunusa ya ce an musguna wa 'ya'yan jam'iyyar a wasu wurare har da kisa, saboda haka hukumar zabe ba ta yi aikin ta yadda ya kamata ba domin ta gaza. Yunusa ya ce shugaban Hukumar zabe ya yi alkawalin kawar da magudin zabe wajen yin amfani da na'urar BIVAS amma kuma akasin haka aka samu a lokacin wannan zaben,saboda haka kwaliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Amma Jamiyyar SDP da ke karkashin shugabancin Alhaji Shehu Gabam , ta ce ta amince da sakamakon zaben Shugaban kasa da Hukumar zabe ta bayyana .
Gabam ya ce abu daya da Jamiyyar SDP za ta yi shi ne shigar da kara akan zabukan yan Majalisun dokokin tarayya inda ya ke ganin 'ya'yan jam'iyyar SDP suna da korafi. Gabam ya ce akwai wurare da dama a wasu jihohi da ba a kyautata wa 'ya'yan jamiyyar su ba, kuma yana ganin haka ba daidai ba ne, domin ba a bi ka'idar da dokar zabe ta shekara 2022 ta gindaya ba.
A lokacin da yake nashi nazari akan sharuddan shigar da kara akan sakamakon zabe,masanin shari'a kuma kwararre a fanin Kundin tsarin mulkin kasa, Mainasara ibrahim Umar ya ce akwai abin dubawa a dokar zabe da abinda Kundin tsarin mulki ya kunsa.
Mainasara ya ce dokar kasa sashi na 6 da 36 da sashi na 230 da sashi 304 sun ba dan kasa dama ta kalubalantar duk wata sanarwa da ta kunshi sakamakon zabe daga kotun farko har zuwa kotun Allah ya isa.
Gwanatocin kasashe da dama irin su Faransa da Ingila har da Kasar Amurka, sun aike wa Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da sakon taya murna amma da sharadin cewa a sa ido akan korafe korafen da yan kasa suka yi kan sakamakon zaben.
Saurari rahoton Madina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5