Zaben Kasar Kenya Ya Fuskanci Cikas

'Yan adawa suna jifan 'yan sanda da duwatsu jiya Alhamis ranar sake zaben shugaban kasa

Jiaya Alhamis arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga ta kawo cikas wa zaben shugaban kasar Kenya da aka sake yi na fitar da shugaban kasa, zaben da 'yan adawa suka kauracewa

Zaben shugaban kasar da aka sake a Kenya ya fuskanci cikas bayan da aka yi arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga a jiya Alhamis, yayin da aka gaza bude wasu rumfunan zabe a yankunan da ‘yan adawa suka fi rinjaye.

Shugaban hukumar zaben kasar, Wafula Chebukati, ya ce an dage zabe a wasu kananan hukumomi hudu a yankunan ‘yan adawa a yammcin kasar ta Kenya, sai gobe Asabar.

Yankunan da aka dage zaben sun hada da Homa Hay da Kisumu da Migora da kuma Siaya saboda dalilai na tsaro.

An samu barkewar rikici a Kisumu, inda aka harbe wani mutum har lahira yayin wata arangama da ta faru tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga, a cewar ‘yan sandan yankin.

Wannan zabe, na zuwa ne sama da watannin biyu bayan da kotu kolin kasar ta soke nasarar da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya samu, saboda kura-kuran da kotun ta ce hukumar zaben kasar ta tafka.

Sai dai duk haka, shi ma wannan zabe ya shiga rudani, domin shugaban ‘yan adawa Raila Odinga ya janye takararsa makwanni biyu gabanin zaben, inda ya yi ikrarin cewa hukumar zaben kasar ba ta yi sauye-sauyen da za su inganta zaben ba, dalilin da ya sa ya yi kira ga magoya bayansa da su kauracewa rumfunan zaben.