Ga dukkan alamu, idan ba a kai zuciya nesa ba, za a shiga rudu a kasar kamaru sanadiyyar takaddamar bayan zaben Shugaban kasa. Wannan ko ya biyo bayan cewa da wani dan adawa ya yi shi ya ci zaben Shugaban kasa, duk kuwa da bai gabatar da hujja ba.
WASHINGTON D.C. —
Da alamar dai wata kura na gab da tashi a kasar Kamaru, inda tsohon Ministan Shari’ar Kasar kuma dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar MRC, Maurice Kamto, ya ce shi ne ya ci zaben Shugaban kasar, ba Paul Biya ba, al’amarin da ya janyo martanin hiukumomin kasar.
Wani jami’I a Kotun Kundin Tsarin Mulki ta kasar Kamaru, Suleiman Alhaji, ya ce bai dace Mr. Maurice ya yi gaban kansa wajen ayyana kansa a matsayin dan takara ba. Haka zalika, Ministan Yada Labaran kasar, Isa Ciroma, y ace Maurice ya saba ka’ida.
Ga wakilinmu, Awwal Garba da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5