Jam'iyar PDP a jihar Yobe da wanda ya yi mata takara gwamnan Adamu Maina Waziri suna zargin wani jami'in gwamnatin Yobe mai suna Zakari Beba da baiwa shugaban hukumar zaben jihar na goro, suna zargin cewa an sanya masa naira miliyan 8 a susun ajiyar sa a bankin Diamond. Daga baya aka sanya masa karin naira miliyan 7 a asusun ajiyarsa dake bankin Zenith, kwanaki uku kafin ayi zabe.
Wakilin sashen Hassan Maina Kaina ya aiko da rahoton cewa, wata kotu a Abuja, karkashin jagorancin mai shari'ar Mojisola Dada ta gaiyaci jami'an bankunan guda biyu daga birnin Damaturu zuwa birnin Abuja domin bada sheda.
Bankunan sun gabatarwa kotu wasu muhimman takardun bayanai na asusun ajiyar da ake magana akai. Dayake amsar tambayar lauyan masu kara, jami'in bankin yace kafin ranar 8 ga watan Afrlun wannan shekara, naira dubu 28 da dari daya da arba'in da uku da kwabo sittin ne kacal a cikin asusun ajiyar. Bayan da aka sanya kudin ne aka cire aka maida asusun ajiyar wani kamfani.
A bangaren sa lauyan dake kare jam'iyar APC da gwamna Ibrahim Geidam, baban lauya Yusuf Ali ya tambayi jami'an bankunan, shin ko banki na daukan hoton duk wanda ya zo zai sanya kudi a asusun ajiya, sai suka amsa da cewa a'a. Ke nan kowa zai iya sanya kudi a kowane asusu ba tare da mai asusun ya sani ba.
Lauyan Adamu Maina Waziri yace tunda mai asusun ajiya ya soma taba kudin, hakan na tabbatar da mai bada cin hanci da mai karba.
Lauyan gwamna Geidam yace al'amarin yana da sarkakiya ainun. Ya bada misalin da cewa, idan aka ce wani abu ya faru a gabas, sai aka kawo sheda daga yamma, ai an saki hanya kwata kwata.
Your browser doesn’t support HTML5