Zaben Ghana: Gagarumin Taron Karshe Na Magoya Bayan Babbar Jam’iyyar Adawa Ta NDC

Lokacin babban taron jam’iyyar NDC a Accra, Ghana

Dubban magoya bayan babbar jam’iyyar adawa ta NDC ne suka hallara a filin wasa na Zurak da ke unguwar Madina, a Accra babban birnin Ghana, domin gangamin karshe na jam'iyyar, a wani yunkuri kafin babban zaben da za a gudanar gobe Asabar, 7 ga watan Disamba

Dan takarar jam'iyyar NDC, John Dramani Mahama ya yi kira ga 'yan Ghana da su kada masa kuri’a domin ya ceto kasar daga matsalar da ta dabaibaye ta.

‘Dan takaran jam'iyyar NDC, John Dramani Mahama lokacin babban taron karshe a Accra, Ghana

Baya ga alkawarin kara saita Ghana, yadda za ta dawo kamar yadda take ko fiye da yadda ya bari a baya, Mr. Mahama ya sake jaddada rage kudin zuwa aikin Hajji da karin hutun karamar Sallah ga Musulman kasar.

Ya ce, “yau idan zaka aikin Hajji, ana biyan $4500, yanzu za mu cire $1000 mu jefar, sai ya koma $3500, yadda yake ada a NDC. Za mu kara muku ‘Holiday’ wato hutu guda a kan Eid-el-Fitr, saboda idan an yi salla yau, a samu ranar hutawa kashe gari.”

Babban taron karshe na magoya bayan jam’iyyar NDC a birnin Accra, Ghana

Haka kuma ya yi gargadi ga masu ruwa da tsaki da su yi adalci, ya ce, “Ina so in gargadi gwamnatin NPP da jami’an tsaron mu, da su gudanar da aikinsu ga al’ummar Ghana yadda ya kamata. Ku kiyaye daga duk wasu munanan ayyuka da ka iya yin barazana ga adalci a wadannan zabukan,”

Magoya bayan jam’iyyar NDC a Ghana

Shugaban jam’iyyar, Johnson Asiedu Nketia, a nasa jawabin ya yi kira da kada ‘yan jam’iyya su yi angulu da kan zabo. Ya ce, “Shugaba Mahama zai koma kan karagar mulki da gagarumin rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Ba za a yaudare mu da yin angulu da kan zabo ba. Za mu zabi shugaban kasa Mahama, da ‘yan takarar mu na majalisar dokoki.

Na yi aiki da ’yan takarar majalisar dokoki 276 na wannan jam’iyya a fadin kasar nan, kuma ina da yakinin cewa za mu dawo kan karagar mulki da gagarumin rinjaye a majalisa.”

Babban Taron Karshe Na Jam’iyyar NDC, Ghana

Wasu magoya bayan jam’iyyar a tsokacinsu ga Muryar Amurka, sun kira ga kowa da ya fito ranar zabe ya kadawa John Dramani Mahama kuri’a.

Gangamin dai ya kasance dama na karshe ga jam’iyyar na yin kira ga ‘yan kasar Ghana kan neman wa’adin komawa kan karagar mulki a zaben da za a gudanr nan da awanni kasa da 24.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Ghana: Gagarumin Taron Karshe Na Magoya Bayan Babbar Jam’iyyar Adawa Ta NDC.mp3