Zaben Fidda gwanin Gwamnonin PDP Sun Yi Sabbin Fuskoki A Siyasar Jihohin Bauchi Da Gombe

Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali.

Zaben fidda gwani na gwamnoni a Jam’iyar PDP a Jihohin Bauchi da kuma Gombe ya samar da sabbin fuskoki a fagen siyasa.

Tsohon Sakataren gwamnatin Jihar, Barrister Kashim Ibrahim shine aka zaba wanda zai yi takarar kujerar gwamna, a yayinda a Jihar Gombe aka zabi Muhammed Jibrin Barde wanda ya yi canjin sheka daga Jam’iyar APC.

Zaben fidda gwanin da ya gudana a Bauchi, ya gudana ne, ba tare da wata hamayya ba, wato kadaran kadahan, inda aka kada masa kuri’u guda dari shida da hamsin da biyar (655 ).

A jawabin da ya gabatar a bayan da aka bayyana sakamakon zaben, tsohon Sakataren gwamnatin Jihar, Barrister Kashim Ibrahim yace yana godiya ga mutanen da suka zabe shi don ganin ya cancanta.

Ku Duba Wannan Ma APC Za Ta Gudanar Da Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa Ranar Lahadi

Shima shugaban Jam’iyar PDP a Jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, yace jama’a sun zabi abinda suke so.

A Jihar Gombe, makwabciyar Bauchi, 'yan takarar guda biyar ne suka fafata a zaben fidda gwanin wanda daga karshe Alhaji Muhammed Barde Jibrin ya yi nasara da kuri’u dari da sittin (160). Shi dai wanda aka zaban masani ne kan harkokin kudi.

A wata sabuwa kuma, ‘ya’yan jam’iyar APC a jihar Bauchi, sun yi taro da kuma yin kira ga uwar jam’iyar ta kasa da kuma a jihar da su yi wa Allah su bari a yi zabe a maimakon dauki dora.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Fidda gwanin Gwamnonin PDP Sun Yi Sabbin Yan Takara A Jihohin Bauchi Da Gombe