‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a jam’iyyyun Democrat da na Republican, na wani yunkuri na karshe a yau Litinin, domin neman goyon bayan masu kada kuri’a a jihohi 11 saboda jam’iyyunsu su tsaida su a matsayin ‘yan takararsu.
WASHINGTON DC —
‘Yan Republican sun fi maida hankalai ne a kudancin kasar, wanda yanki ne da ke da kashi biyu cikin uku na wakilan da za su kada kuri’a babban zaben da ake wa inkiya da “Super Tuesday”
Hamshakin mai kudin nan Donald Trump, wanda ke gaba a karbuwa a jam’iyyar Republican, zai yi gangami a Virginia da Georgia, yayin da Sanata Marco Rubio da ya fito daga Florida zai yi kamfen dinsa Arkansas.
Shi kuwa Sanata Ted Cruz ya maida hankali ne a jiharsa ta Texas, wato inda ya ke neman goyon bayan akalla wakilai 155 cikin 600 da suka fito daga jihar.