Kamar yadda ta ce za ta yi, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta garzaya kotu, inda ta gabatar da takardun kararta kan ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasa, a maimakon gwaninta Alhaji Atiku Abubakar, wanda ta ce shi ya ci zaben.
Da ya ke karin bayani kan kalubalantar ayyana Buhari a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasa da Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta yi, daya daga cikin lauyoyin jam’iyyar PDP Mike Ezekhome y ace, “Mu na da kwararan hujjoji da mu ka dogara da su don karbar nasarar mu a mayarwa Atiku Abubakar shaidar lashe zabe.”
PDP ta kai karar ne a kotun daukaka kara, inda ake kyautata zaton daga nan shari’ar za ta yi ta tafiya har ta kare a kotun koli, kamar yadda tsarin yak e.
Sakataren PDP, Sanata Umar Tsauri, ya ce jam’iyyarsu sam ba ta amince da kuri’un da a ka sanar shugaba Buhari ya samu ba, ya na mai zargin a wasu wajajen ma rubuta kuri’a a ka yi. Shi ma kakakin kamfen na jam’iyyar, Buba Galadima, ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa muddun za a yi shari’ar adalci, to labudda PDP za ta koma fadar Aso Rock.
Amma a daya gefen kuma, Ministan Shari’a kuma Attoni-Janar din Najeriya, Abubakar Malami, ya ce a shirye gwamnatin APC ta ke ta kare nasarar da ta yi a zaben Shugaban kasa a kotu; ya kara da cewa zuwa kotu ba bakon abu ba ne ga Shugaba Buhari.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5