Masana harkokin siyasar dai sun ce daga wurin zaɓen fidda ƴan takara na jam,iyyu ne ake samun shugaba na gari da zai shugabanci al'umma ko kuma akasin haka,
Kwamred Ibrahim Tungan Wawa Mai Sharhi ne akan harkokin Siyasar Duniya yace kasahen da suka ci gaba jam'iyyu na zaɓen ƴan takarane akan cancanta ba wai ra'ayin wani ba.
A nashi bayanin, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi Ɗan Majalisar Dattawan Nigeria Mai Wakiltar Arewacin Jihar Neja da a yanzu yake buƙatar ganin jam'iyya ta APC ta sake bashi damar tsayawa takara dan komawa Majalisar yace indai za' a yi adalci baya da shakku sake komawa majalisa bisa la'akari da aikin da ya yi wa al'ummarsa.
Shima dai gwamna Abubakar Sani Bello dake neman Jam' iyyar APC ta bashi damar tsayawa takarar neman kujerar majalisar dattawan daga Arewacin Nejan yace duk da APC ta samu karbuwa sosai ga Jama'a, a lokacin zaben fidda gwani lamarin na bata ruwa.
A yanzu dai manyan jam'iyyun siyasar dake gogayya da juna a Nigeria wato APC da PDP sun bada tabbacin yin adalci a lokacin zaɓuɓɓukan fidda ƴan takarar. Yayinda hankalin 'yan Nigeria ya karkata ga masu zaben fidda ƴantakara na ja,miyyun siyasar Nigeriar.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5