ZABEN 2023: Jam'iyyun Siyasa Marasa Tasiri Na Samun ‘Yan Takara

Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)

Alamu na nuna wasu jam’iyyu da a baya ba su da tagomashi na samun ‘yan takara takarar mukaman zaben 2023 mai zuwa.

A zabukan baya da su ka hada da na 1999 akwai jam’iyyun da ba sa samun tasiri don rashin ‘yan takara masu goyon bayan jama’a.

Daga cikin irin wadannan jam’iyyu akwai PRP ta Malam Aminu Kano da SDP da Moshood Abiola ya yi takara a inuwar ta a zaben 1993.

Kazalika a kan iya samun jam’iyyun na tsaida ‘yan takarar gwamna a wasu jihohi amma sai su buge da marawa dan takarar babbar jam’iyya a zaben shugaban kasa.

Sai dai a wannan karon dan takarar gwamna na PRP a Katsina Imran Jino ya ce sun yunkuro don sauya wannan dabi’a da ke takura tabarmar dimokradiyya.

Hakanan shi ma dan takarar majalisar dattawa a Kebbi ta tsakiya a inuwar NNPP Injiniya Farouk Umar na nuna kwarin guiwar nasara a takarar ko ba kudi da manyan ‘yan siyasa ke amfani da su wajen samun kuri’a.

Duk da haka ‘yan manyan jam’iyyu da ke barazanar gocewa jam’iyyun na cewa ko ma dai a kasa za su kauce amma su na sa ran wanzuwar jam’iyyar a taraiya.

Dogon lokacin da a ke da shi zuwa babban zaben a febrerun badi, zai iya gajiyar da ‘yan siyasar kudi inda masu bayanai da cusa manufa za su fi cin gajiya.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kananan jam'iyun siyasa na kara samun karbuwa-3:00"