Ibrahim Babangida ya bayyana wannan ne da ya gana da wasu magoya bayan mataimakin shugaban kasar a inuwar kungiyar tafiyar Osibanjo Grassroots Organisation.
‘Yan kungiyar a karkashin jagorancin Ojo Foluso sun ziyarci Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya a gidansa da ke garin Minna, jihar Neja a ranar Alhamis.
Tsohon shugaban ya ce ya san Osinbajo sosai a matsayin mutumin kirki wanda ya amince da dorewar Najeriya a matsayinta na tsinciya daya da kuma iya jagorancin sa, saboda haka yana bukatar sa da ya tsaya tsayin-daka, ya nemi takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na shekarar 2023 domin kuwa kasar na bukatar mutanen kirki irin sa.
Tsohon shugaban ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta gari mai dauke da mutanen kirki wadda ke neman wanda ya fahimce ta da jama’ar ta domin tattaunawa da su a koda yaushe.
A cewar IBB “Na san mataimakin shugaban kasar nan da kyau. Mutumin kirki ne. Mutumin da ya yi imani da Najeriya, wanda jama’a za su iya sauraronsa, ya zaburar da su.” “Ya dace ayi aiki da mutum irin wannan. Mu na bukatar mutumin kwarai ya rike Najeriya.”
A cewar Janar IBB, Osinbajo mutumi ne da yake da kishin kasa, yace dole ne duk wanda za a bar wa shugabanci, ya fahimci halin al’umma kafin ya iya jagorantar su.
Babangida yace ya yarda ya zama da kungiyar ne domin ya san Osinbajo ya na da abin da ake bukata wajen zama shugaba na gari.
Babangida ya aika da sakon fatan alherinsa ga Osinbanjo ta hannun tawagan kungiyar tare da bukatar sa da ya jajirce akan aniyar sa, duk da yake ya san cewar akwai jan aiki agabansa.
A wani bangaren Dan majalisar tarayya kana tsohon mataimaki na musamman ga Osinbanjo Honarable Hafizu Kawu ya yaba da kalaman tsohon shugaban inda ya ce a matsayinsu na masu kaunar Najeriya wadanda suka sadaukar da kansu a kan cigaba da gina kasar duk lokacin da suka yi kalamai na yabo ko kuma suka ga cancantar wani da ya jagoranci kasar abin a yaba musu duba da irin ayyuka iri na musammam da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauko na cigaban kasa wadansu sai nan da shekara biyu zuwa uku ko fiye da haka kafin a kammala su kamar layin dogo, harkan wutar lantarki da dai sauransu abu ne da ke bukatar wanda ya kware kuma ya sansu kuma mataimakin shugaban kasar da shi aka fara ya san abubuwa da yawa da gwamnatin nan ke yi.
Sai dai Ya zuwa wannan lokaci mataimakin shugaban kasar bai bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar zabe ba, amma kuma tuni wasu kungiyoyi daga sassan Najeriya suka fara masa kamfe da zummar ganin ya shiga takarar da za’ayi domin neman shugabancin kasar kuma wannan aniyar ta su tayi karo da ta jagoran APC Bola Ahmed Tinubu kuma tsohon mai gidan Osinbajo a siyasance wanda ake ganin zai tsaya takarar zaben mai zuwa.
A cewar masanin siyasa a Najeriya Honarable Sa’idu Gombe cancanta ya kamata yanzu a duba ba wai banbance banbance dake tsakanin jam’iyyu ya a ko uban gida ba kuma mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbanjo Mutum ne da ke da ilimi na tafi da mulki musammam idan aka yi la’akari da cewa duk lokacin da shugaban kasa ke tafiye tafiye shi ya ke tafiyar harkokin kasar ta yi gaba kuma ana samun ‘yan sauye sauye daga irin shugabancin da yake yi, kuma wannan halama ce da ke nuni da cewa idan aka bashi shugabancin kasar zai iya.
Yanzu abin jira a gani dai shine waye zai maye yan kasar za zaba yayin da ya rage yan watanin a shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daka kan kujerar mulkin kasar.
Saurari sauti cikin Rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim
Your browser doesn’t support HTML5