Al’ummar jihar Nasarawa sun fara tofa albarkacin bakinsu, kan irin ci gaba da suke bukatar shugabannin da zasu jagoranci ragamar mulkin jihar zasu kawo, don su sami walwalar rayuwa.
Jihar Nasarawa na daga cikin jihohin da zasu samu sabuwar gwamnati, bayan gwamna mai ci, Umaru Tanko Almakura ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas.
Al’ummar jihar na cewa suna bukatar wanda zai hada kan jama’a ne, da kawo sauye-sauye masu inganci don su sami sassaucin rayuwa.
Injiniya Abdullahi Sule, wanda tuni ya kaddamar da yakin neman zabensa, yace zai fuskanci batun kafa masana’antu, samarwa matasa ayyukan yi, da habaka hanyoyin shigar kudade a jihar.
Kan batun tsaro kuwa, kwamadan Civil Defence a jihar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari, yace sun shirya tsaf don dakile matsalolin tsaro, kafin zabe, lokacin zabe da ma bayan zabe.
Your browser doesn’t support HTML5