Masu ruwa da tsaki da talakawa a jihar Jigawa na ci gaba da bayyana albarkacin bakin su dangane da alkawarin dan takarar shugabancin najeriya na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yayi na ci gaba da aikin samar da filin noman rani mai fadin fiye da kadada miliyan daya a jihar a lokacin daya kai ziyarar neman kuri'a jihar a litinin din nan.
Baya ga alkawarin bunkasa ayyukan noman rani wadda ke karkashin kulawar hukumar raya koramun Hadejia da Jamare da gwamnatin marigayi shugaba Shagari ta kammala kashin farko a shekarun 1980, dantakarar na Jam'iyyar PDP yace zai sake gina hanyar mota daga Gaya zuwa Jahun zuwa Kafin Hausa ta bulle yankin Gashuwa a jihar Yobe, kana da wadda ta tashi daga kwanar Dumawa a jihar Kano zuwa Babura ta hade da Jamhuriyar Nijar.
Tsohon gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido wanda ya jagoranci tawagar Atikun Zuwa Jigawan ya yi tanbihi game da wannan gagarumin aiki da cewa, adashen da zasu zuba ke nan a matsayinsu na jiha da suke kyautata zaton dan takarar jam'iyar PDP zai cika.
Bayan maraba da wannan batu na raya noman rani da hanyoyi, talakawan na Jigawa na ne karin ababen habaka rayuwarsu da suka hada da ilimi da inganta rayuwar talakawa.
Shi kuwa a nasa bangaren, Hon Nasiru Garba Dantiye dake neman kujerar majalisar wakilan Najeriya daga mazabar Garki/Babura a jam'iyyar ta PDP yayi alkawarin taka rawar data kamata domin kwalliya ta biya kudin sabulu game da alkawuran da aka yiwa talakawa.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Kwari
Your browser doesn’t support HTML5