ZABEN 2015: Yau Ce Ranar Zabe a Najeriya

An yi zanga-zangar rashin yarda da jinkirta zabe.

Bayan da aka dage ranar zaben makonni shida da suka gabata, yau ranar ta zo to ko menene masu kada kuri'a yakamata su lura dasu domin kuri'unsu su yi tasiri?

Zaben Najeriya da za'a fara yau da alama zai yi zafi ainun musamman tsakanin shugaban kasa Jonathan da babban abokin hayayyarsa Janar Muhammad Buhari.

Kodayake akwai 'yan takara da dama amma duk dantakarar da ya samu fiye da kashi hamsin cikin dari da kuri'un da aka kada kuma ya samu kashi ashirin da biyar cikin dari na jihohi ashirin da hudu to shi ne zakara. To amma kada a yi mamaki idan zaben shugaban kasa ya shiga zagaye na biyu.

A karon farko a kasar za'a yi anfani da naurar tantance masu kada kuri'u. Naurar zata tabbatar cewa wanda ya bayyana a rumfar zabe da kati shi ne aka yiwa rajista domin naurar zata fitar da sunansa har ma da hotonsa. Ita dai hukumar zabe ko INEC tace kashi tamanin cikin dari na mutanen da ta yiwa rajista sun karbi katunansu na din-din-din.

Akwai wasu abubuwan da masu kada kuri'a yakamata sa sani su kuma lura dasu.Kwamishanan zabe na jihar Adamawa Alhaji Baba Abdu Yusuf yace za'a yi anfani da kuri'a mai launin ja wajen zaben shugaban kasa. Kuri'a mai launin baki ita ce ta majalisar dattawa. 'Yan majalisar wakilai kuma suna da mai launin kore. Yakamata jama'a su kula da launukan.

Akwatunan zaben ma suna da launi daban daban. Ja shi ne na shugaban kasa. Baki shi ne na majalisar dattawa kana kore kuma na majalisar wakilai.

Hukumomin tsaro sun bukaci jama'a su sa ido kan wadanda ka iya zuwa rumfunan zaben da wata manufa daban. Mutane su kaujewa zuwa rumfar zabe da jaka ko makami. An dauki matakin ne sabili da yin la'akari da irin halin da kasar ke ciki na rashin zaman lafiya da kuma yadda muggan mutane ke shiga cikin jama'a suna ta'adanci.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Yau Ce Ranar Zabe a Najeriya - 3' 31"

.