Furucin wasu 'yan siyasa suna tsoratar da mutane da firgitar dasu lamarin da ya sa suka soma komawa jihohinsu.
'Yan arewacin Najeriya da ma na kudancin kasar suna komawa inda suka fito. Misali 'yan arewacin Najeriya dake zaune a yankin Niger Delta suna barin wurarensu alatilas suna komawa arewa sabili da kalamun mutanen yankin. Akwai fargabar cewa zabukan ka iya zuwa cikin tashin hankali.
Wasu da Muryar Amurka ta zanta dasu domin sanin dalilinsu na barin inda suke zama sun ce zasu koma gida saboda rikice-rikicen siyasa. Wani Magaji Maiduguri yace 'yanuwansu da suke tare dasu suna tsorata su. Yace kashi biyu cikin uku duk sun tafi.
Kasumu Hamisu yace 'yan asalin wurin da suke zama suna batun cewa za'a yi rikici a wannan zaben. Sabili da haka iyayensu sun gargadesu da su koma gida.
Haka ma wasu 'yan kudancin Njeriya da suka kwashe shekaru da dama suna zaune a arewa suna kwashe kayansu suna komawa gida domin fargabar abun da ka biyo bayan zabe kamar yadda aka yi a shekarar 2011.
Ga bayanin Lamido Abubakar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5